Gwamnatin Kano zata ɗauki tsatstsauran mataki a kan masu yin sana’ar achaba

0
15

Gwamnatin Jihar Kano ta fara aiwatar da matakai na musamman domin dakile sake bayyana masu achaba a cikin birnin Kano, duk da dokar haramta hakan da aka dade da sanya wa.

Hakan ya biyo bayan rahotannin da hukumomi suka samu na cewa babura masu kafa biyu sun fara komawa titunan birnin Kano don yin sana’ar achaba, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma da jami’an tsaro saboda yiwuwar amfani da su wajen aikata laifuka.

A wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa bayanan leƙen asiri sun tabbatar da yawaitar zirga-zirgar babura a wasu unguwanni, har ma da wasu mutanen da ba a san su ba da ke shigowa yankuna suna amfani da babura da sunan achaba.

Sanarwar ta ce gwamnati ta tura ƙarin jami’an tsaro zuwa kananan hukumomi 44 na jihar domin ganin an dakile duk wata barazana ta tsaro daga kowace fuska.

Gwamnati ta kuma sake jaddada cewa duk wanda aka kama yana gudanar da sana’ar achaba a Kano, zai fuskanci hukunci ba tare da wani rangwame ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here