Gwamnatin Kano ta nemi a dena tsangwamar masu ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki

0
7

Gwamnatin Jihar Kano ta gudanar da bikin Ranar Yaki da Cutar Mai Karya Garkuwar Jiki ta Duniya, tare da jaddada aniyar ta, ta ci gaba da yaki da cutar duk da raguwar tallafin yaƙi da cutar daga kungiyoyin duniya.

Taron, wanda aka gudanar ƙarƙashin jagorancin Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano da Hukumar Yaki da Cutar ƙanjamau ta Jihar Kano (KSACA), ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu, hukumomin lafiya, da masanan fannin cutar.

Taken bikin na bana ya jaddada buƙatar ci gaba da ɗaukar nauyin yaki da cutar a matakai daban-daban.

A rahoton bana, an bayyana cewa Kano na da mutane 37,825 masu ɗauke da cutar mai karya garkuwar jiki, tare da mutuwar 551. 

An yi wa mutane 607,720 gwaji, aka gano 2440, na ɗauke da cutar kuma aka fara bayar da magani ga 2388. Haka kuma an gwada mata masu juna biyu 238,495, inda 34 aka gano suna dauke da cutar, kuma an kula da su har suka haifi jarirai ba tare da kamuwa ba. An gwada yara 31,277, aka gano 68, duk ana kula da su.

Gwamnatin tace ta ƙara kuɗin da take warewa domin yaki da cutar zuwa Naira biliyan 2, tare da sakin sama da miliyan 500 don siyan kayan gwaji, inganta aiki da lantarki mai amfani da hasken rana a hukumar kula da cutar, gina sabuwar cibiyar kula da yara masu cututtuka a asibitin Murtala, da kuma sauran muhimman ayyuka.

Bugu da ƙari, sama da mutane 4200 masu cutar mai karya garkuwar jiki da 600 daga cikin marayu da yara masu rauni sun sami tallafin inshorar lafiya ba tare da biyan kuɗi ba.

Gwamnatin Kano ta jaddada kudirin ta na kare al’umma da kawo ƙarshen cutar mai karya garkuwar jiki kafin shekara ta 2030, tare da kira ga jama’a su ci gaba da yin gwaji, shan magani, da guje wa wariya ga masu cutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here