Gwamnatin Kano ta jan kunnen masu yaɗa labarai na ƙarya a kan tsaron jihar

0
9

Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta tabbatar wa mazauna jihar cewa akwai tsaro a Kano, babu wata barazana da ya kamata ta tada hankulan jama’a.

Wannan tabbaci ya fito ne daga bakin mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, bayan taron kwamitin tsaro na jihar da aka gudanar ranar Lahadi tare da manyan hukumomin tsaro.

A cewar sanarwar, babu wani sahihin bayanan leƙen asiri da ke nuna akwai barazana ga zaman lafiya ko tsaron jihar. Gwamnati ta bayyana damuwa kan yaɗuwar labaran bogi da wasu ke ƙoƙarin watsawa domin haifar da tsoro da rikice-rikice a tsakanin jama’a.

Gwamnatin ta ce tana aiki kafada da kafada da hukumomin leƙen asiri, rundunonin tsaro da kuma al’umma, tare da ƙara tsaurara matakan tsaro domin tabbatar da cewa babu wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya. 

Gwamnati ta bukaci jama’a su kwantar da hankula, su guji yada labaran karya musamman ta kafafen sada zumunta, domin hakan na iya kawo matsalolin da za su janyo hukunci daga kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here