A makamanciyar wannan rana ce shekaru 13 da suka gabata akalla mutane 100 suka rasa rayukan su, yayin da 135 suka samu raunuka a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a babban masallacin Juma’a da ke cikin birnin Kano.Â
Gwamnan jihar Kano, na wancan lokaci Rabiu Musa Kwankwaso, ne ya tabbatar da hakan yayin da yake ganawa da manema labarai bayan ya kai ziyarar jaje ga wadanda ake jinya a asibiti.
Harin, wanda ake zaton kungiyar Boko Haram, da kaiwa ya haÉ—a da tayar da bamabamai uku da kuma bude wuta kan masu ibada, a kusa da fadar Sarkin Kano.
Harin na daga cikin hare-haren Æ´an ta’adda da ya tayar da hankalin al’umma a Najeriya saboda girman asarar rayukan da aka samu.


