Kamfanin mai na ƙasa NNPCL ya sanar da rage farashin man fetur a Abuja da Lagos.
Rahotonni sun tabbatar da cewa a ranar Alhamis farashin ya sauka daga Naira 910 zuwa Naira 900 a Lagos, sannan daga Naira 945 zuwa Naira 940 a Abuja.
Raguwar ta zo ne makonni uku bayan matatar Dangote ta rage farashin man zuwa Naira 828 kan lita, lamarin da ya yi tasiri kasuwar mai.


