Lakurawa sun kashe jami’an hukumar shige da fice da ƙone masallaci a Kebbi

0
10

Wasu da ake zargin ’yan ta’addan Lakurawa ne sun kai mummunan hari kan ofishin Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS) da ke Bakin Ruwa, kusa da iyakar Maje a ƙaramar hukumar Bagudo, jihar Kebbi, inda suka kashe jami’ai uku.

Lamarin ya faru a daren Alhamis, da misalin ƙarfe 12 na dare, lamarin da ya tayar da hankalin al’ummar yankin. 

Majiyoyi sun ce jami’an sun gudu don neman mafaka a masallaci, amma maharan suka bi sahun su, suka bude musu wuta, sannan suka banka wa masallacin wuta. 

Rahotanni sun nuna cewa har ma an yi amfani da makamai masu linzami a harin.

Bayan haka, maharan sun kuma ƙona gidajen jami’an da ke kusa da wurin. Wannan hari ya zo ne kasa da wata guda bayan kashe jami’in Kwastam da kona motocin gwamnati a yankin Maje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here