Japan ta fara sayar da injin da ke yi wa mutum wanka 

0
6

Ƙasar Japan ta fara sayar da wani injin zamani da ke yi wa mutum cikakken wanka ta hanyar shiga ciki a kwanta bayan shaharar sa da ya yi a lokacin baje kolin duniya da aka gudanar a Osaka.

Wata mai magana da yawun kamfanin Science, wanda ya ƙera na’urar, ta shaida wa AFP cewa mutane sun yi dogayen layuka domin gwada samfurin injin a lokacin baje kolin da ya ja hankalin fiye da mutum miliyan 27 a cikin watanni shida da aka gudanar.

Na’urar, wacce aka lakaba mata suna “injin wankin ɗan adam”, na aiki ne ta hanyar sanya mutum cikin wata rufaffiyar akwati, inda injin ke fesa ruwa da sabulu da sauran sinadarai a jikin mutum, ba tare da wani jujjuyawa irin na injin wanki ba. A lokaci guda kuma ana kunna kiɗa domin nishadantar da mai amfani da shi.

Mai magana da yawun Science, Sachiko Maekura, ta bayyana cewa shugaban kamfanin ya fara tunanin ƙera irin wannan na’ura tun yana ƙaramin yaro, bayan ganin irin ta a baje kolin Osaka na shekarar 1970.

Ta ce na’urar ba wai tana tsaftace jiki kaɗai ba, har ma tana nazarin wasu alamomin lafiya irin su bugun zuciya domin tabbatar da jin daɗin mai amfani.

Rahotannin kafofin yada labaran Japan sun bayyana cewa farashin injin ɗaya zai kai Yen miliyan 60, kwatankwacin sama da Naira miliyan 500 a kuɗin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here