Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC) ta gayyaci tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), domin gudanar da tambayoyi kan wasu al’amura da ba a bayyana ba.
Malami, ne ya tabbatar da gayyatar a safiyar Juma’a ta hanyar wani sako da ya wallafa a shafin sa na Facebook.
Ya ce: “Wannan shi ne tabbatar wa cewa an gayyace ni zuwa hukumar EFCC. A matsayi na na ɗan kasa mai bin doka da kuma yaƙi da rashin gaskiya, zan halarci wannan gayyata.
Ya ƙara da cewa zai rika sanar da al’umma duk wani ci gaba da ya shafi batun, domin tabbatar da gaskiya.
Malami ya taka rawar gani a gwamnati a matsayin ministan shari’a tun daga ƙarshen 2015 zuwa Mayu 2023 a zamanin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
A halin yanzu, Malami mutum ne mai tasiri a jam’iyyar ADC, tare da zama ɗaya daga cikin masu don neman takarar gwamnan jihar Kebbi.


