Mayaƙan Boko Haram sun nemi aikin soja da ɗan sanda a Najeriya–Wase

0
26

Tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Ahmed Idris-Wase, ya bayyana cewa an taɓa gano sunayen ’yan Boko Haram da sauran ƴan ta’adda a jerin wadanda ake shirin dauka aiki a rundunar Soji da ’Yan Sanda.

Wase ya yi wannan magana ne a wani zaman musamman na majalisar da aka gudanar kan matsalar tsaro a Najeriya. Ya ce irin wannan shigar baragurbi cikin hukumomin tsaro babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaron kasa.

Ya yi kira ga ’yan siyasa da ke bada takardun shaidar ba da izinin daukar aiki su daina cusa miyagu, su rika tabbatar da mutanen kirki ne kawai ake kaiwa mukaman tsaro.

Har ila yau, Wase ya bayyana cewa Arewa ta Tsakiya tana da kusan kaso 52% na matsalolin tsaro a kasar. Ya ce lamarin ya shafe shi kai tsaye domin ya rasa dan uwa da suruki a hare-haren ’yan ta’adda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here