Majalisar Dattawa zata bawa ƴan Najeriya damar mallakar bindiga saboda rashin tsaro

0
23

 Ƴan majalisar dattawa na duba yiwuwar bai wa ‘yan kasa nagari damar mallakar bindiga domin kare kai, yayin da Mataimakin Shugaban Majalisa, Barau Jibrin, ya bukaci karin hadin kai tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya wajen yaki da ta’addanci.

Ƴan majalisar sun bayyana hakan yayin da suka yi gargadi cewa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na janye jami’an ‘yan sanda daga manyan mutane ya zo a “mummunan lokaci,” yana barin su cikin hatsarin hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Sanata Aliyu Wamakko da Sanata Tahir Monguno sun ce ‘yan siyasa na kara zama manyan manufofin miyagu, musamman yayin ziyartar mazabu, don haka janye masu tsaro zai iya haifar da mummunar illa. Majalisar Dattawa ta yanke shawarar tunkarar Shugaban Kasa da hukumar ’yan sanda domin sake duba matakin.

A Majalisar Wakilai, Ahmed Idris Wase ya yi gargadin cewa ‘yan siyasa da jami’an gwamnati na fuskantar barazana kai tsaye, musamman ganin yadda garkuwa da mutane ke ƙaruwa a manyan hanyoyi.

Idan za’a iya tunawa dai shugaban ƙasa Tinubu, ya bayar da umurnin janye ƴan sanda daga bayar da kariya ga manyan mutane don tunkarar matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.

Ya nemi a mayar da yan sandan zuwa guraren da ake fama karancin jami’an tsaro musamman ƙauyuka da sauran su, sannan ya umarci jami’an NSCDC su riƙa bayar da kariya ga manyan mutane a maimakon yan sanda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here