Hisbah ta daƙile yunkurin safarar wasu ƴan mata a Kano

0
11

Rundunar Hisbah ta Kano ta samu nasarar dakile wani yunkurin safarar ƴan mata da aka taho da su daga jihar Jigawa zuwa Kano, inda wata mata mai bin addinin Kirista, daga jihar Oyo, take karɓar yaran daga wani mutum mai suna Habibu Idris, a kan kuɗi Naira dubu 10, kan kowane mutum ɗaya.

Mataimakin babban kwamandan rundunar Hisbah Dr. Mujahideen Aminuddeen, ne ya bayyana hakan, yana mai cewa lamarin ya faru a ƙaramar hukumar Fagge.

Yace al’ummar Fagge ƙasan gada ne suka kaiwa Hisbah rahoto bayan hayaniya ta ɓarke tsakanin Habibu Idris, da Basirat Tijjani, akan kuɗin mota da take bashi in ya kawo yara.

Da farko yana karɓar Naira dubu 10 a kan duk mutum guda, sai dai yanzu yace sai an bashi Naira dubu 15, kuma hakan ne ya haifar da rikici tsakanin su, har hankalin al’umma ya kai wajen da kuma fahimtar laifin da ake kokarin aikatawa.

Yaran da za’a yi safarar sun hadar da Kubairiyya Amadu, yar shekaru 14, sai Rukayya Umar, shekaru 17, da Rashida Usaini, Shekaru 14, dukkan su daga jihar Jigawa.

Zuwa yanzu dai Hisbah, ta miƙa lamarin zuwa ga hukumar dake yaƙi da safarar mutane ta ƙasa don faɗaɗa bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here