Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana jimaminsa a sakamakon rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
A wata sanarwa da Babban Jami’in Yaɗa Labaran sa, Edwin Olofu, ya fitar, Ganduje ya bayyana marigayin a matsayin babban masanin ilimi da ƙaunar lumana, wanda rayuwar sa ta yi tasiri ga musulmi a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.
Ya ce Sheikh Dahiru Bauchi ya kasance mutum mai tawali’u, jajirtacce wajen yaɗa ilimi da ɗabi’a ta gari, abin koyi ga kowane bangare na al’umma, na addini, na siyasa da na al’ada.
Ganduje ya miƙa ta’aziyyar sa ga Masarautar Bauchi, Gwamnatin Jihar Bauchi, iyalan marigayin, almajiran sa dake faɗin duniya, da daukacin mabiya Tijjaniyya.
Ya roƙi Allah Ya gafarta masa, Ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdaus.


