Fitacccen malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya rasu a cikin daren da ya gabata, kamar yadda wata majiya mai tushe ta tabbatar wa RFI Hausa.
Majiyar ta ce za a gudanar da jana’izar sa a gobe Juma’a a garin Bauchi ƙarƙashin jagorancin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh.
Muna fatan Allah ya gafarta masa da sauran al’ummar musulmi.


