Ƴan bindiga sun sace manoma da masu juna biyu a jihar Neja

0
7

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da manoma 20, ciki har da mata masu juna biyu da yara, a wani sabon hari da ya faru a Unguwan-Kawo da ke cikin gundumar Erena, karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Rahotanni daga mazauna yankin sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 4 na yammacin Laraba, yayin da manoman ke aikin girbi a gonar shinkafa da ke kimanin mita 500 kacal daga garin Erena, inda sansanin sojoji yake.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunan sa ya bayyana cewa ɗan’uwansa yana cikin wadanda aka yi garkuwa da su. Ya ce al’ummar yankin sun shiga halin firgici ganin yadda hare-haren ke ta ƙaruwa a kananan hukumomin jihar.

Wannan hari na zuwa ne kwanaki shida bayan sace dalibai da ma’aikata sama da 200 daga makarantar St. Mary Primary and Secondary School da ke Papiri, a karamar hukumar Agwara.

Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce rundunar za ta bincika rahoton domin tabbatar da gaskiyar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here