Hukumar tsaron farin kaya DSS ta bayyana wa kotu cewa Tukur Mamu, wanda ake zargi da shiga tattaunawar ‘yan ta’adda da al’umma a harin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna a 2022, ya karɓi Naira miliyan 50 daga shugaban ƙungiyar ƴan ta’addan da suka kai harin.
Shaidar DSS ta ce kuɗin sun fito ne daga kudaden fansa da iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su suka tara.
Mamu yana fuskantar tuhuma da dama, ciki har da karɓar kuɗin fansa, hulɗa da kuɗaɗen ta’addanci, hana aikin kwamitin CDS na tattaunawa da ’yan bindiga, da musayar bayanai da kakakin Boko Haram.
A zaman shari’ar da aka ci gaba da ita a ranar Talata, shaidar DSS ta ce ƙungiyar ta nemi Mamu ya koya musu yadda ake buɗe shafin yanar gizo domin gudanar da aikace-aikacen su.
A wani bangare kuma, Mamu ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya, yana ƙalubalantar ayyana shi “ a matsayin ɗan ta’adda” da Ministan Shari’a ya yi, yana mai cewa ana tuhumar sa ne kawai, kuma dokar ƙasa ta ba shi damar a ɗauke shi da rashin laifi har sai an tabbatar.
Kotun ta ɗage shari’ar har zuwa 23 ga Fabrairu, 2026 domin ci gaba da sauraren hujjojin bangarorin biyu.


