Ceto daliban Kebbi ba nasara ba ce–Atiku

0
8

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin tarayya kan yadda aka saki ɗaliban makarantar Maga da aka sace a Jihar Kebbi, yana mai cewa wannan ba abin murna ba ne, illa dai nuna yadda rashin tsaro ya tsananta a ƙasar nan.

A wata sanarwa da ya fitar, Atiku ya ce sakin ƴan matan “ba abin murna ba ne”, domin hakan kawai na nuni da yadda ’yan bindiga ke gudanar da harkokinsu cikin sauƙi, suna tattaunawa da jami’an gwamnati ba tare da tsoro ba.

Atiku ya yi wannan jawabi ne bayan Bayo Onanuga, mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan sadarwa, ya bayyana cewa DSS da sojoji sun bi sawun masu garkuwa da daliban a kai a kai har suka samu damar tattaunawa da su ba tare da biyan kudin fansa ba.

Sai dai Atiku ya bukaci gwamnati ta bayyana dalilin da yasa, idan har suna ganin ’yan ta’addan, ba a kama su ba, balle a tarwatsa sansanonin su.

Ya ce wannan bayani na gwamnati yana nuni da cewa ’yan bindiga sun zama “wata sabuwar gwamnati”, suna sace mutane, suna tattaunawa, suna kuma tsallakewa ba tare da hukunci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here