Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya bayyana cewa an sake kubutar da wasu ɗalibai 11 na makarantar St Mary da aka sace a kwanan nan.
A tattaunawar sa da BBC, gwamnan ya ce jami’an tsaro tare da haɗin kan al’umma ne suka gano yaran a wani daji, cikin wani samame da suka kai domin ceton su.
Sai dai ya ƙi bayyana yadda suka tabbatar da sahihancin waɗanda aka kuɓutar.
Bago ya musanta jita-jitar da ke cewa an sace ɗalibai fiye da 300, yana mai cewa makarantar bata samar da cikakken bayani ba, duk da gargadin da jami’an tsaro suka basu game da barazanar tsaro kafin faruwar lamarin.
Gwamnan ya kuma ce an buɗe rijistar musamman a ƙaramar hukumar Agwara domin iyayen da ’ya’yansu suka ɓace su rubuta sunayensu. Amma zuwa yanzu, iyaye 14 kacal ne suka zo suka yi rajista.
A cewar sa, dukkan makarantun kwana da ke yankunan da ake ganin suna da matuƙar haɗari, musamman a Papiri, za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai an tabbatar da cikakken tsaro.


