Ƴan bindiga sun sace bindigar ɗan sanda bayan kashe shi a Zamfara
Ƴan ta’adda kashe wani jami’in ɗan sandan tafi da gidan ka, a wani harin kwanton-ɓauna da ‘yan bindiga suka yi a kauyen Adabka, dake ƙaramar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata, inda rahoton masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya bayyana cewa jami’in wanda aka turo daga Ilorin ya bar matsugunin sa a Adabka yana kan hanyar sa zuwa kauyen Tibis domin siyan kayayyakin amfani.
A cewar majiyar tsaro, ‘yan bindigar da ke ɓoye a cikin daji a wajen kauyen sun bude masa wuta, suka kashe shi nan take sannan suka tafi da bindigar aikin sa.
Jami’an tsaro da aka tura wajen faruwar lamarin sun ɗauko gawar marigayin, tare da kai ta cibiyar lafiya ta Adabka domin rubuta bayanai da ɗaukar sauran matakai.


