Wike ya dakatar da Danlami Hayyo kan batun rufe makarantun Abuja

0
21

Hukumomin Birnin Tarayya sun bayyana cewa labarin da ake yaɗawa kan umurtar makarantu su rufe zuwa ranar 28 ga Nuwamba ba gaskiya ba ne, tare da cewa babu wani mataki da aka ɗauka da ya shafi rufe makarantu a wannan lokacin.

Mai magana da yawun Ministan birnin, Lere Olayinka, ya sanar da cewa Minista Nyesom Wike ya bayar da umarnin dakatar da Sakataren Ilimin Abuja, Dakta Danlami Hayyo, kan wannan  jita-jita.

Haka kuma, Shugabar Ma’aikata mai rikon kwarya, Nancy Sabanti Nathan, ta samu umarnin ɗaukar mataki kan Daraktar Sashen Makarantu, Aishatu Sani Alhassan, bisa saɓa ka’idojin aikin gwamnati.

Gwamnati ta roƙi iyaye, ɗalibai da shugabannin makarantu su yi watsi da jita-jitar, tana mai tabbatar da cewa jadawalin karatu yana nan babu canji.

Ministan yace ana ɗaukar matakan tsaro domin kare lafiyar ɗalibai da sauran mazauna birnin, ciki har da sake farfaɗo da aikin sintirin tsaro domin kula da zaman lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here