Talauci ne ya janyo matsalolin tsaron arewa–Gwamnan Jigawa

0
8

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana cewa talauci shi ne babban tushen matsalolin da ke addabar Arewacin Najeriya, musamman bangaren tsaro.

A cikin wata sanarwa da kakakin sa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar, gwamnan ya yi wannan bayani ne a Kaduna yayin bikin cika shekaru 25 da kafuwar kungiyar tuntuɓa ta Arewa ACF da kuma kaddamar da Asusun Tallafin ta.

Namadi ya ce duk da cewa rashin tsaro na ci gaba da zama babbar barazana, dole ne a waiwayi ainihin dalilan da ke haifar da shi, musamman talauci da ƙarancin yalwatuwar tattalin arziki.

Ya jaddada cewa Arewa na da isassun albarkatu, ƙasar noma mai faɗi, da ƙarfi wajen samar da ma’aikata, wanda ya kamata a yi amfani da su wajen ƙirƙirar arziki da kawar da talauci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here