Babbar Kotun Jihar Kano da ke Miller Road, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji, ta ci gaba da sauraron shari’ar Hamisu Baita Dandago, matashin da ake tuhuma da kashe ɗan makocin sa, Suyudi, tare da cire masa ido a shekarar 2023.
A zaman kotun na yau, lauyoyin gwamnati Barista Ummi Lawan da Barista Bello Isa, sun gabatar da wanda ake tuhuma, inda aka ci gaba da sauraron bayanin sa.
Lauyan dake kare wanda ake tuhuma, Barista Ogbobula, ya gabatar da Hamisu Baita domin ya yi bayani, tare da kawo wani da mahaifin sa, Sani Baita Dandago. Sani ya shaida wa kotu cewa ɗan sa na fama da matsalar tabin hankali lokaci-lokaci. Sai dai ya gaza tabbatar wa kotu ko ya sanar da ‘yan sanda wannan matsalar tun lokacin da aka kama shi.
Bayan jin bayanin shaidar, lauyan dake kare Hamisu ya nemi kotu ta ba su damar kawo likita domin tantance lafiyar hankalin wanda ake tuhuma, inda kotu ta amince da hakan.
Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji ya dage ci gaban shari’ar zuwa ranar 22 ga Janairu, 2026, tare da umartar jami’in gidan gyaran hali, Mahmud Datti Abubakar, da ya mayar da Hamisu Baita gidan gyaran hali domin ci gaba da tsare shi.
An fara gurfanar da Hamisu Baita a gaban kotu tun shekarar 2023 bisa zarginsa da sace yaron makocinsu, Suyudi, ya kai shi wani kango a unguwar Sani Mai Nage, inda ake zargin ya kashe shi sannan ya cire masa ido.


