Gwamnonin arewa sun shirya taron gaggawa kan matsalolin tsaro a yankin

0
10

Gwamnonin jihohin Arewa 19 sun shirya gudanar da wata muhimmiyar ganawar gaggawa a ranar Asabar, 29 ga Nuwamba, domin tattauna matsalar tsaro da ta tsananta a yankin.

Wannan bayani ya fito ne daga Peter Ahemba, babban mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Nasarawa kan harkokin yaÉ—a labarai, yayin da yake zantawa da Daily Trust.

A cewar sa, za a gudanar da taron ne a Kaduna, tare da halartar manyan shugabannin gargajiya daga sassa daban-daban na Arewa. Ahemba ya ce manufar taron ita ce samar da matsaya É—aya wacce za ta taimaka wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar yankin.

Ya bayyana cewa, gwamnatin Nasarawa ta riga ta É—auki matakai tun kafin taron, ta hanyar gudanar da nata taron tsaro na gaggawa domin dakile duk wata barazana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here