Ganduje zai ƙirƙiro sabuwar rundunar Hisbah a Kano

0
21

Tsohon Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya tabbatar da cewa zai nemo wa kusan jami’an Hisbah 12,000 da yace an kora daga aiki, a jihar mafita ta dindindin, tare da yiwuwar kirkiro kungiyar sa kai mai kama da Hisbah domin su ci gaba da aikin addini da zamantakewa.

Ganduje ya bayyana hakan ne yayin karɓar rahoton kwamitin da ya nada domin nazarin batun. Jami’an da abin ya shafa sun haɗa da manya da ƙananun ma’aikatan Hisbah.

Kwamitin dai yana ƙarƙashin jagorancin tsohon Kwamandan Hisbah na Kano, Dr. Harun Ibn Sina, tare da tsohon Daraktan KAROTA Baffa Babba Dan Agundi, da wasu malamai.

A cikin bayani na ƙarin haske, Dr. Harun Ibn Sina ya ce sabon tsarin Hisbah mai zaman kanta ba zai zama mai cin karo da hukumar Hisbah ta gwamnati ba, sai dai zai yi aiki ne tamkar wasu ƙungiyoyin agaji da wa’azi, domin tallafa wa al’umma cikin natsuwa da tsarin doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here