Dabarun sojojin Najeriya sun gaza magance matsalolin tsaro–Gwamnan Kebbi

0
10

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana cewa tsarin da rundunar sojin Najeriya ke amfani da shi wajen yaki da rashin tsaro “ba ya aiki yadda ya kamata,” yana mai kira da a sake fasalin dabarun yaƙi da rashin tsaro.

Idris ya yi wannan jawabi ne lokacin da ya karbi bakuncin Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, a Birnin Kebbi, bayan sace dalibai mata na makarantar GCGSS Maga da ’yan bindiga suka yi.

Gwamnan ya kuma bukaci a binciki dalilin janye jami’an tsaro daga makarantar mintuna kafin afkuwar harin, tare da tambayar yadda ’yan bindiga sama da 500 ke yawo a babura ba tare da an dakatar da su ba.

> “Mun samar da motocin aiki sama da guda 100, amma tsarin tsaro ba ya aiki. Idan mun san za a bar ’yan mata haka, da mun rufe makarantar gaba daya,” in ji shi.

Ya ce hare-haren da ake yi a jihohin Kebbi, Niger da Kwara na nuna cewa “wani bangare na neman dagula gwamnati,” wanda ya bukaci Majalisar Wakilai ta dauki mataki.

Kakakin Majalisar, Abbas Tajudeen, ya jajanta wa al’ummar Kebbi, tare da bada tallafin Naira miliyan 30 ga iyalan wani jami’in da aka kashe da kuma wasu da abin ya shafa. Ya ce majalisar za ta goyi bayan kokarin gano daliban da aka sace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here