Ƴan bindiga sun sake kai hari a jihar Kwara 

0
16

Al’ummar ƙauyen Isapa da ke kusa da Eruku, a ƙaramar hukumar Ekiti ta Jihar Kwara, sun shiga tashin hankali bayan da wasu ‘yan bindiga sun kai sabon hari inda suka sace mutum 11, ciki har da mata masu juna biyu, masu shayarwa da ƙananan yara.

Wannan harin dai ya faru ne da yammacin Litinin, misalin ƙarfe 6 na yamma, kwana guda bayan sakin wasu masu ibada da aka yi garkuwa da su a wata coci da ke yankin.

Shaidu sun bayyana cewa maharan, kimanin 20 zuwa 30, sun afka cikin garin suna harbi kan mai uwa da wabi, abin da ya sa mazauna yankin suka watse domin neman mafaka. 

Wani shugaban al’umma ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana cewa mutum 11 da aka sace sun haɗa da mutane bakwai daga gida ɗaya. 

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kwara, CP Adekimi Ojo, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce yana kan hanyar sa ta zuwa Isapa domin gudanar da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here