NNPP ta nesanta kanta daga shirin Kwankwaso na gudanar da wasu tarukan siyasa

0
11

Jam’iyyar NNPP ta nemi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da al’umma su yi watsi da niyyar gudanar da wasu sabbin taruka da Kungiyar Kwankwasiyya ƙarƙashin jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta sanar, tana mai cewa matakin ba bisa ka’ida ba ne.

A cikin wata sanarwa da Sakataren jam’iyyar na Ƙasa, Ogini Olaposi, ya fitar a ranar Litinin, jam’iyyar ta bayyana cewa taron da kotu ta umarta a gudanar sun rigaya sun kammalu, don haka babu wani abu da ya rage.

NNPP ta ce ta samu labarin wata wasika da tawagar Kwankwaso ta aikewa INEC, inda suka bayyana cewa za su gudanar da sabbin taruka da babban taron jam’iyya na ƙasa daga 25 ga Nuwamba zuwa Janairu 2026.

Sai dai jam’iyyar NNPP ta jaddada cewa Kwankwasiyya ba ta da hurumin gudanar da taro a madadin ta, kasancewar yarjejeniyar haɗin gwiwar da aka kulla a lokacin zaɓen 2023 ta ƙare tun tuni.

Jam’iyyar ta kuma jaddada cewa Kwankwaso an kori Kwankwaso daga cikin ta saboda zargin cin dunduniyar NNPP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here