Kotu ta yi watsi da ƙarar da ICPC ta shigar da shugaban hukumar zaɓe ta jihar Kano

0
7

A yau Litinin ne, babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yi watsi da ƙarar da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Dangogin su ta ƙasa (ICPC) ta shigar kan wasu manyan jami’an hukumar Zaɓe ta Kano (KANSIEC).

Wadanda ICPC ta gurfanar sun haɗa da:

Farfesa Sani Lawal Malumfashi, Shugaban KANSIEC

Anas Muhammed Mustapha, Sakataren Hukumar

Ado Garba, Daraktan Kuɗi

ICPC ta zarge su da aikata laifuka 10 da suka shafi badakalar Naira biliyan 1.02 a lokacin gudanar da zaɓen kananan hukumomi na 2024.

An tsara fara gurfanar da su a gaban kotu a ranar Litinin, a ƙarƙashin shari’a mai lamba FHC/ABJ/210/2025, amma zaman bai yiwu ba saboda wadanda ake tuhuma ba su bayyana ba.

Lauyan ICPC, Enosa Omoghibo, ya shaida wa kotu cewa an tanadi zaman domin gabatar da tuhume-tuhume, amma waɗanda ake zargi da aikata laifin ba su halarta ba.

Sai dai lauyan KANSIEC, M.A. Magaji (SAN), ya bayyana cewa babu sahihin isar da takardun tuhuma ga wadanda ake tuhuma, wanda hakan a cewar sa ya saba da ka’idar tabbatar da hurumin kotu.

Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta dage zaman zuwa 24 ga Nuwamba don ba da damar isar da takardu yadda ya dace da kuma tabbatar da zuwan bangarorin shari’ar.

A sabon zaman da aka gudanar a ranar Litinin, sai dai har yanzu wadanda ake tuhuma ba su bayyana a kotu ba, lamarin da ya sa Mai Shari’a ta yi watsi da shari’ar gaba ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here