Gwamnatin Jihar Bauchi ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare, sakandare da manyan makarantu a faɗin jihar, ciki har da na gwamnatin tarayya da masu zaman kansu, saboda matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a sassan ƙasar nan.
Wannan matakin na zuwa ne bayan rahotannin hare-haren Boko Haram da karuwar sace-sacen ɗalibai a jihohin Niger da Kebbi, da kuma harin da ya yi sanadiyyar mutuwar ’yan sanda biyar a Sabon Sara da ke Darazo, kamar yadda rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar a ranar Lahadi.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi, Jalaludeen Usman, ya fitar, gwamnati ta ce an ɗauki matakin ne bayan tattaunawa mai zurfi da hukumomi daban-daban, domin kare rayukan ɗalibai, malamai da ma’aikatan makarantu.
Sanarwar ta ce duk da cewa rufe makarantu na iya kawo cikas ga tsarin karatu, gwamnati ba za ta yi wasa da rayuka ba.
Gwamnati ta roƙi iyaye, malamai, masu makarantu da sauran jama’a su kwantar da hankalinsu tare da yin hadin kai yayin da ake ci gaba da nemo mafita. Ta kuma bayyana cewa tana aiki kafada da kafada da jami’an tsaro domin tabbatar da komai ya dawo daidai cikin gaggawa.


