Ƴan siyasa ne ke rura wutar rashin tsaro a Najeriya–Uzor Kalu

0
13

Sanata Orji Uzor Kalu mai wakiltar Abia Ta Arewa ya bayyana cewa ƙaruwar hare-haren ta’addanci, sace-sacen mutane da kuma rufe makarantu a sassan ƙasar nan ba abin da ke jawo hakan face wata dabara ta siyasa da wasu ke amfani da ita domin matsa wa gwamnati lamba.

Kalu ya bayyana haka ne a shirin Sunday Politics na Channels TV, inda ya ce irin waɗannan matsalolin yakan ƙaru ne a duk lokacin da zaɓe ke gabatowa. Ya yi nuni da cewa an sha ganin irin wannan yanayi a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, yana mai cewa wasu ’yan siyasa suna ɗaukar ƴan ta’adda daga waje domin tada tarzoma.

Sanatan ya ƙara da cewa akwai hannun wasu ’yan ƙasa da kuma wasu daga ƙasashen waje da ke ƙoƙarin tayar da hankali a Najeriya, musamman ganin yadda aka fara maganar zaɓen 2027.

Sai dai ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu na ɗaukar matakai domin shawo kan matsalolin tsaro, yana mai cewa shugaban ƙasar ya nuna kwarin guiwa wajen tunkarar kalubalen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here