Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin janye jami’an ‘yan sanda da ke tsaron manyan mutane domin mayar da su kan muhimman aikin su na samar da tsaro a cikin al’umma.
Umarnin ya fito ne bayan wani muhimmin taron tsaro da Shugaba Tinubu ya jagoranta a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja, tare da manyan hafsoshin tsaro ciki har da Shugaban Sojin Ƙasa, Lt. Janar Waidi Shaibu; Shugaban Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke; Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun; da Darakta-Janar na DSS, Tosin Adeola Ajayi.
A cewar umarnin, duk wani babban mutum da ke buƙatar kariya daga yanzu zai nemi jami’an tsaro daga Hukumar NSCDC, domin bai wa ‘yan sanda damar komawa aiki a yankunan da ake buƙatar su sosai, musamman cikin karkara.
Gwamnatin tarayya, ta bayyana cewa ƙarancin jami’an ‘yan sanda a wurare da dama yana kawo cikas wajen bai wa jama’a isasshen tsaro, musamman a wannan lokaci da ƙalubalen tsaro ya ƙaru.
Shugaba Tinubu ya kuma amince da ɗaukar karin ‘yan sanda 30,000, tare da haɗin gwiwa da jihohi domin inganta cibiyoyin horas wa a fadin ƙasa.
Wannan sanarwar ta fito ne daga Bayo Onanuga, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Labarai da Dabaru, a ranar 23 ga Nuwamba, 2025.


