Tinubu na jagorantar muhimmin taro a kan tsaro

0
8

Tinubu na jagorantar muhimmin taro a kan tsaro 

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na jagorantar wani muhimmin taron da ya shafi sha’anin tsaro tare da Shugabannin Rundunonin Tsaro, Sifeto Janar na ‘Yan Sanda, Daraktan DSS, da kuma shugabannin sauran hukumomin leƙen asiri a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.

A cewar bayanan da suka fito daga Fadar Shugaban Kasa, taron ya mai da hankali kan nazarin rahotannin tsaro na baya-bayan nan da kuma ɗaukar matakai na gaggawa domin kwantar da tarzoma da kariya ga rayukan ‘yan ƙasa, sakamakon ƙaruwar hare-haren ƴan ta’adda a yan kwanakin nan.

Cikin sakon da ya wallafa a shafin sa na Facebook, shugaba Tinubu ya ce yana karɓar rahotanni kai tsaye yayin da yake ba da umarnin cewa jami’an tsaro su yi aiki da a kan lokaci, amfani da dabaru domin dawo da tabbataccen zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.

Tinubu ya jaddada cewa ba za a lamunci duk wani abu da zai tayar da hankali ko kawo barazana ga zaman lafiyar ƙasa ba, domin doka za ta yi aikin ta a kan duk masu tada zaune tsaye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here