Gwamnatin Yobe ta rufe makarantun jihar saboda barazanar tsaro

0
9

Gwamnatin Jihar Yobe ta dauki matakin rufe dukkan makarantun sakandiren kwana a fadin jihar, sakamakon karuwar barazanar tsaro da kai hare-hare kan makarantu a yankunan Arewa.

Wata sanarwa da Daraktan YaÉ—a Labaran Gwamnan Jihar, Mamman Mohammed, ya fitar ta bayyana cewa an dauki matakin ne domin kare rayukan É—aliban da ke makarantu. A cewarsa, gwamnatin ba za ta yi jinkiri ba wajen daukar duk wani mataki da ya shafi tsaron É—alibai ba.

Rufe makarantun ya biyo bayan sabon harin da ’yan bindiga suka kai a makonnin baya a jihohin Neja da Kebbi, inda aka sace dalibai daga makarantun kwana. Lamarin ya tada hankalin a’lumma a arewa.

Sanarwar ta ce an cimma matsayar ne bayan taron tsaro na musamman da Gwamna Mai Mala Buni ya jagoran ta, inda aka duba yadda ake iya kara tabbatar da tsaron makarantu a jihar.

Rufe makarantun zai fara aiki nan take, har sai an tabbatar da ingantuwar yanayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here