Fafaroma Leo XIV, ya nemi a gaggauta sakin ɗalibai da malamai sama da 300 da aka sace a hare-haren makarantun Najeriya, wanda ya zama ɗaya daga cikin manyan sace-sacen dalibai a tarihin ƙasar nan.
A jawabin sa bayan gabatar da wata addu’a, Fafaroma ya nuna “babbar damuwa da alhini” kan sace ɗalibai, malamai, da mambobin coci a Najeriya da Kamaru, yana mai roƙon a ceto su cikin gaggawa. Ya kuma jajanta wa iyalan waɗanda ke cikin halin tsaka mai wuya.


