Ba zan bari a cigaba da jubar da jinin ƴan arewa ba—Tinubu

0
11

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnati ba za ta zuba ido Arewa ta ci gaba da fama da ta’addanci ba, da zubar da jinin al’umma.

Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin taron cika shekaru 25 da kafa kungiyar tuntuɓa ta Arewa ACF wanda ya gudana a jihar Kaduna.

 Tinubu, ya bayyana hakan ta bakin Kakakin Majalisar wakilai Tajudeen Abbas, wanda ya wakilce shi.

Tinubu ya ce ya karɓi mulkin Najeriya cikin matsanancin rashin tsaro, amma gwamnatinsa na aiki tukuru don kawo ƙarshen ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran su.

Ya bayyana cewa ci gaban Najeriya ba zai yiwuwa ba idan Arewa na cikin rikici, yana mai jaddada bukatar shugabanni su yi aiki da gaskiya, su kula da talakawa, su kuma dawo da ɗabi’un al’umma masu kyau.

Tinubu ya ce akwai damar farfado da tattalin arzikin yankin, musamman da shirin haƙo da mai daga Kolmani.

Ya nuna kwarin guiwa cewa Arewa za ta samu tsaro, ta farfado da tattalin arzikin ta, ta kuma ci gaba da zama ginshiƙin ci gaban kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here