Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana jin daɗinsa kan sakin mutum 38 da aka sace a lokacin harin da aka kai Cocin Christ Apostolic Church (CAC) da ke Eruku, ƙaramar hukumar Ekiti ta jihar.
A wata sanarwa da Rafiu Ajakaye, Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna, ya fitar, an bayyana cewa nasarar ceto waɗanda aka sace ɗin ta samu ne sakamakon jajircewar Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya jagoranci dukkan matakan kwato mutanen.
Ajakaye ya ce Shugaba Tinubu ya nuna jajircewa wajen magance matsalolin tsaro, inda ya soke wata tafiya da ya shirya zuwa taron G20 a Afirka ta Kudu domin mayar da hankali kan lamarin sace-sacen da ya faru a jihohin Kwara da Kebbi. Ya kuma bayar da umarnin tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankunan da abin ya shafa.


