Ƴan bindigar da suka sace ɗalibai sun fara fuskantar fushin mu–Rundunar sojin ƙasa

0
11

Shugaban Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa-Masataki (JTF North West), Manjo Janar Warrah Idris, ya bayyana cewa ’yan bindiga sun fara jin matsin lambar da dakarun suka tsananta domin ceto ɗaliban makarantar St. Mary’s Catholic School da aka sace a Papiri, ƙaramar hukumar Agwara, Jihar Neja.

Janar Idris ya fadi hakan ne bayan ya kai ziyarar duba halin da ake ciki a yankin da lamarin ya faru, inda ya samu cikakken bayani daga Manjo Janar CR Nnebiefe, kan yadda ake gudanar da atisayen hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro.

A cewar mai magana da yawun Operation Fansan Yamma, Kyaftin David Adewusi, rundunar ta kuduri aniyar ganin an kubutar da dukkan ɗalibai cikin koshin lafiya.

Janar Idris ya jaddada cewa babu inda ’yan bindigar za su samu mafaka, yana mai umartar dakarun su ci gaba da matsa kaimi ba tare da sassauci ba har sai an ceto kowace ɗaliba.

Ya kuma tabbatar wa sojojin da cewa ana samar da dukkan kayan aiki da tallafi da ake bukata domin tabbatar da nasarar aikin ceton.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here