Rundunar ‘yan sandan Jihar Gombe ta karyata wani labarin da ya yaɗuwa a kafafen sada zumunta da ke cewa an kai hari zuwa cocin ECWA da ke Kashere, karamar hukumar Akko, tare da sace mutane.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Buhari Abdullahi, ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana rahoton a matsayin “karya”, yana mai jaddada cewa babu wani hari da ya faru a wurin.
Wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa an mamaye coci tare da yin garkuwa da mabiya addinin kirista, lamarin da rundunar ta ce ba gaskiya ba ne.
A cewar ƴan sandan, jami’an da ke Kashere sun tuntubi wani dattijo daga cikin shugabannin cocin. Dattijon, wanda ya kasance a cikin coci kuma ya tabbatar musu cewa komai ya gudana lafiya ba tare da wani tashin hankali ba.
Rundunar ta kuma ce jami’an tsaro sun kasance a harabar cocin tun daga safe domin gudanar da tsare-tsaren tsaro na yau da kullum.
Rundunar ta bukaci jama’a da su guji yada labaran bogi tare da tabbatar da sahihancin bayanai kafin yada su.


