Ƴan bindiga sun kashe jami’an ƴan sanda 5 a Bauchi

0
8

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Bauchi ta tabbatar da kashe jami’an ta biyar a wani harin kwantan-bauna da ’yan bindiga suka kai musu a garin Sabon Sara da ke karamar hukumar Darazo.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, mai magana da yawun rundunar, CSP Ahmed Wakil, ya ce lamarin ya faru ne a yayin da jami’an ke gudanar da sintirin gani-da-ido domin shawo kan yiwuwar rikicin manoma da makiyaya a yankin.

Harin ya yi sanadin mutuwar DSP Ahmad Muhammad (SID), ASP Mustapha Muhammad (10 PMF), Inspecta Amarhel Yunusa (10 PMF), Inspecta Idris Ahmed (10 PMF) da Corporal Isah Muazu (AKU). 

Haka kuma Inspecta Isah Musa da Inspecta Yusuf Gambo sun jikkata.

Babban jami’in ɗan sanda na Darazo, SP Auwalu Ilu, ya jagoranci ƙarin jami’ai zuwa wurin domin ceto waɗanda suka ji rauni tare da kai gawarwakin jami’an da suka rasa rai zuwa asibiti.

Rundunar ta ce an kashe wasu daga cikin waɗanda suka kai harin, tuni an fara aikin bincike da fatattakar dukkan waɗanda suka aikata laifin.

CSP Wakil ya tabbatar da cewa duk masu hannu a wannan ta’asa za a kama su tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here