Uwar gidan shugaban haramtacciyar kungiyar masu neman kafa kasar Biafra IPOB, Uchechi Okwu-Kanu, ta soki lauyoyin mijinta saboda rashin sanar da ita kafin a tura Nnamdi Kanu daga hannun DSS zuwa gidan gyaran hali na Sokoto bayan yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai.
Ta ce ta samu labarin ne bayan awa uku, da tura shi Sokoto duk da cewa wasu da suka ziyarci mijinta sun san haka, amma suka gaza faɗa mata sannan suka garzaya kafafen sada zumunta suna wallafa labarin.
Okwu-Kanu ta bayyana hakan a matsayin rashin kwarewa, tana gargadin lauyoyin da su gyara aikin su.


