Ata ya mayar da martani kan wasikar gargaɗi da aka aike masa

0
11

Karamin Ministan Gidaje da Bunƙasa Birane, Rt. Hon. Yusuf Abdullahi Ata, ya bayyana cewa ya samu labarin wata wasikar gargadi da ake ikirarin an rubuta masa ta hanyar kafafen sada zumunta, kafin ta iso gare shi ta hanya da ta dace.

A wata sanarwa da ya fitar, Ata ya ce hakan ba daidai ba ne, ganin cewa bai dace Ministan Tarayyar Najeriya ya fara ganin irin wannan takarda a kafafen sada zumunta kafin a mika masa a hukumance ba.

Ministan ya kara da cewa wasikar ba ta fayyace kalaman da ake zarginsa da furtawa ko wani aiki da ya saba ƙa’ida ba, lamarin da ya sanya bai ga dalilin mayar da martani kai tsaye ba.

A cewarsa, yana da cikakkiyar damar bayyana ra’ayinsa a matsayinsa na ɗan Najeriya bisa tanadin kundin tsarin mulki, kuma bai taɓa yin wata magana da ke nuna wajabcin bin ra’ayin wani mutum a madadin jam’iyya ba. Ya ce dukkan kalamansa na siyasa yana yi ne a matsayinsa na mutum mai ‘yancin fadin albarkacin baki.

Ata ya kuma jaddada cewa yana nan daram a matsayin mamba nagari na jam’iyyar APC, tare da goyon bayan manufofin gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. 

Ministan ya kammala da fatan cewa za a karɓi bayaninsa cikin mutuntaka da girmamawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here