Ƴan sanda sun kama masu yiwa ƴan ta’adda safarar abinci da gyaran bindiga a Kwara

0
10

Rundunar ‘Yan Sanda da Hukumar DSS a jihar Kwara sun kama wani mutum daga Makurdi, Jihar Benue, wanda ake zargin yana gyaran bindigogi ga ‘yan bindiga da ke addabar al’umma a Eruku, cikin Karamar Hukumar Ekiti.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Adekimi Ojo, ya bayyana haka bayan taron majalisar tsaro ta jihar, inda ya ce an kuma kama wasu da ake zargin suna kai wa ‘yan bindiga abinci, man fetur da magunguna a maboyarsu.

Ojo ya bayyana cewa majalisar ta nuna damuwa kan yadda yada bayanan tsaro a kafafen sada zumunta ke shafar yaki da ta’addanci. Ya ce duk da haka an yaba wa sabbin jami’an tsaro da aka tura Kwara bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ya kara da cewa an samu cigaba wajen samun bayanan sirri da kuma korar ‘yan bindiga daga wasu maboyarsu, musamman a Ifelodun, ta hanyar kai hare-haren sama.

Kwamishinan ya ce jami’an tsaro na cigaba da bin sawun wadanda suka kai harin coci a Eruku, tare da kokarin ceto wadanda aka yi garkuwa da su. A cewar sa, an amince da gudanar da hadin gwiwar sintiri a sassan jihar yayin da ake shirye-shiryen bukukuwan ƙarshen shekara.

Majalisar ta gargadi jama’a su guji yin ayyukan dare da duk wani abu da ka iya saka su cikin hadari, tare da neman rahoton duk wani motsi da ake zargi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here