Gwamnatin jihohin Katsina da Filato sun umarci a rufe dukkan makarantu bayan ƙaruwa hare-haren ‘yan bindiga da suka yi wa cibiyoyin ilimi barazana a yankin Arewa maso Yamma.
A Katsina, Kwamishinan Ilimi na Firamare da Sakandare, Yusuf Jibia, ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin kare rayukan dalibai da malamai, musamman a yayin da ake aiwatar da sabon tsarin tsaron makarantun jiha. Ya ce dukkan makarantu da ke ci gaba da jarrabawa suma sun shiga tsarin rufewar, har sai an kammala binciken tsaro a yankunan da aka gano suna cikin hatsari.
Haka kuma, a Plateau, mai magana da yawun hukumar ilimi a matakin farko SUBEB ta jihar, Richard Jonah, ya sanar da cewa za’a rufe manyan makarant daga Asabar 22 ga Nuwamba, yayin da firamare da makarantun kwana da jeka ka dawo za su rufe daga Litinin 24 ga Nuwamba.
Ya ce matakin na ɗan lokaci ne amma wajibi, domin hana yiwuwar hare-hare da tabbatar da tsaron al’umma.
Matakin rufe makarantun ya biyo bayan sace daliban sakandare a Kebbi da Neja, abin da ya ƙara tayar da hankalin jama’a da hukumomi a arewa.


