Hukumar Zakka ta Jihar Zamfara ta bayyana cewa ta kammala dukkan shirye-shirye domin aurar da marayu 200, a wani shiri na tallafa wa marasa galihu.
Sakataren hukumar, Malam Habibu Balarabe, ne ya tabbatar da hakan, yana mai cewa an gudanar da cikakken bincike da tantancewa kafin zaɓar wadanda za su ci gajiyar shirin, domin tabbatar da cewa auren ya kai ga wadanda suka fi bukata.
An tsara gudanar da bikin auren ne a ranar Litinin, 23 ga Nuwamba, 2025, a harabar hukumar da ke Gusau.
A cewarsa, hukumar za ta ba wa amaren kayayyakin tallafi da kayan amfani na gida domin sauƙaƙa musu da kuma tabbatar da zaman lafiya a sabuwar rayuwarsu.


