Babu izinin mu aka sake buɗe makarantar da aka sace ɗalibai–Gwamnati

0
15

Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana damuwarta kan sace dalibai da ma’aikata na Makarantar Katolika ta St Mary’s da ke Papiri, dake Karamar Hukumar Agwara.

Ƴan bindiga ne suka kutsa makarantar tsakanin ƙarfe 2 zuwa 3 na dare a ranar Juma’a, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da malamai.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin jihar, Abubakar Usman, ya fitar, ya ce an samu bayanan sirri tun da fari cewa akwai barazanar tsaro a yankunan Neja ta Arewa, wanda hakan ya sa gwamnati ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun kwana da dakatar da ayyukan gine-gine a yankin.

Sai dai, a cewar sa, makarantar ta sake bude wa ba tare da neman izini ko sanar da gwamnati ba, duk da gargadin da aka bayar.

Ya ce umarnin gwamnatin ya kasance don kare rayukan ɗalibai da malamai, musamman ganin cewa barazanar tsaro na karuwa a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here