Wasu ’yan ta’adda sun farmaki Makarantar Katolika ta St. Mary’s da ke kauyen Papiri a Karamar Hukumar Agwara ta Jihar Neja, inda suka yi awon gaba dalibai da ma’aikata da ba a san yawan su ba.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru a daren jiya, kuma majiyar Daily Trust ta ce ’yan ta’addan sun shiga makarantar tare da sace dalibai da dama.
Wani na kusa da cocin Katolika ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa makarantar tana tattara cikakken bayanin wadanda aka sace kafin fitar da sanarwa.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce zai fitar da cikakken bayani a kan wannan lamari daga baya.
Haka zalika, Shugaban Sashen Bala’i da Agaji na Karamar Hukumar Agwara, Ahmed Abdullahi Rofia, ya tabbatar da harin ta wayar tarho, yana mai cewa an kai farmakin ne tsakanin ƙarfe 2:00 na dare zuwa 3:00. Ya ce har yanzu ana tantance yawancin daliban da ma’aikatan da aka sace.
Wannan hari ya zo ne mako guda bayan makamancinsa da ya faru a Maga, Jihar Kebbi, inda aka sace dalibai 25, lamarin da ya ƙara tsananta damuwa kan tsaron makarantun Arewa.


