Ƴan fashi sun kai hari ƙaramar hukumar Rimin Gado

0
11

Wasu ƴan fashi da makamai sun kai hari a babban shagon Isa Mai Dusa da ke Gulu, cikin Karamar Hukumar Rimin Gado, Jihar Kano, a daren Juma’a.

Shugaban Karamar Hukumar, Hon. Muhammad Sani Salisu Jili, ya tabbatar da lamarin, ga Arewa Updates, yana mai cewa maharan huɗu ne a kan babura biyu, ɗauke da bindigu, suka dirar wa shagon suka sace kuɗi.

A cewar sa, wata yarinya ta ji rauni yayin gudun tsira sakamakon firgicin harbin bindiga da ƴan fashin suka yi.

Jili ya bayyana cewa jami’an tsaro sun bazama domin kamo masu laifin, tare da tabbatar da cewa za a cafke su nan ba da jimawa ba.

Ya kuma shawarci mazauna Gulu da Rimin Gado su kwantar da hankalinsu, yana mai musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewa hare-haren ‘yan ta’adda ne suka afka wa yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here