Rashin tsaro ya janyo rufe makarantu a jihar Kwara

0
8

Gwamnatin Jihar Kwara ta umurci rufe dukkan makarantu a wasu kananan hukumomi huɗu saboda karuwar hare-haren ƴan ta’adda a kwanakin baya-bayan nan.

A Bokungi, karamar hukumar Edu, an kashe mutane uku yayin harin ranar Laraba. Wannan lamari ya biyo bayan harin da aka kai cocin Eruku a karamar hukumar Ekiti, inda mutane biyu suka mutu, tare da sace wasu 30.

Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakan tsaro a makarantu, ciki har da makarantu masu ɗakin kwana a Irepodun, domin kare ɗalibai daga barayi da ke iya amfani da su a matsayin kariya daga jami’an tsaro. Kuma za a ci gaba da rufe makarantu har sai an tabbatar da tsaro.

Kafin yanzu ‘yan bindiga sun kai hari makarantar GGCSS Maga a Kebbi, inda suka kashe jami’i ɗaya suka sace ɗalibai 25. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here