Manoma a Jihar Taraba na fuskantar mummunar asara sakamakon faduwar farashin amfanin gona, musamman masara da shinkafa. Rahotanni sun nuna cewa mafi yawan manoma ba za su iya dawo da rabin kudin da suka kashe wajen noma ba.
Daily Trust, ta rawaito cewa a Jalingo, Yau Aliyu ya ce gonar masarar sa ta lashe Naira 1,400,000 daga lokacin shuka zuwa girbi. Amma ya samu buhuna 30 na masara kacal, kuma da farashin buhu É—aya ya tsaya a Naira 20,000, jimillar kudin da zai samu bai wuce Naira 600,000 ba. Wannan ya jefa shi cikin asarar Naira 800,000, ya kuma ce hakan ya hana shi shirin yin noman rani a bana.
Shi kuma, Nuhu Dauda ya bayyana cewa ya samu riba ne kawai daga gyada da waken soya, yayinda ya dawo da kusan kashi 40% na zuba jari a masara da shinkafa. Ya ce ya saka kusan Naira 3,000,000 a noman damina, amma farashin kasuwa ya ruÉ—e shi saboda masara da shibk suna kai tsakanin Naira 20,000 zuwa Naira 28,000 kacal a kasuwa.
Manoman sun zargi gwamnatin tarayya da shigo da shinkafa da masara, abin da suke ce ya yi sanadin karyewar farashin amfanin gona a kasuwa.
Sun ce irin wannan shigo da kayayyaki zai iya karya noman cikin gida, sun kuma bukaci gwamnonin Arewa su tashi tsaye wajen tallafa wa manoma domin kar a bar harkar noma ta durkushe.


