Kwamishinan ’Yan Sanda na Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya kai ziyarar aiki zuwa ƙananan hukumomin Shanono da Tsanyawa domin duba yadda jami’an tsaro suka bazu a yankunan da ke kan iyakar Kano da Katsina.
Ziyarar ta biyo bayan karuwar matsalolin tsaro da suka hada da sace mutane da satar shanu da ake dangantawa da wasu ’yan bindiga da ke shigowa daga jihohi makwabta.
A lokacin da yake duba jami’an tsaron da aka tura yankin da kayan aikin da aka ƙara wa, CP Bakori ya yaba wa Rundunar Hadin Gwiwa (JTF) saboda irin jajircewar da suke nunawa wajen kare al’umma.
Ya kuma bukaci jami’ai da su ƙara kaimi, su kasance cikin shiri a kowane lokaci domin dakile duk wata barazana.
CP Bakori ya tabbatar wa jama’ar Kano cewa rundunar ’yan sanda na aiki ba dare ba rana domin tabbatar da zaman lafiya. Ya ce al’umma su ci gaba da ba da rahoton duk wani abin da suke zargi domin taimaka wa jami’an tsaro wajen magance laifuka.
Kwamishinan ya kuma gode wa Gwamnatin Kano, shugabannin ƙananan hukumomin yankin, da al’umma bisa goyon baya da hadin kai da suke baiwa jami’an tsaro, yana mai cewa hakan na da muhimmanci wajen tabbatar da kwanciyar hankali.
Rundunar ’Yan Sandan Kano ta ce za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da shan alwashin ci gaba da shawo kan duk wani sabon kalubalen tsaro.


