Kotu ta samu Nnamdi Kanu da aikata laifin ta’addanci

0
7

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke wa Nnamdi Kanu, jagoran kungiyar IPOB, hukunci kan tuhumar ta’addanci ta farko daga cikin tuhuma bakwai da ake masa.

A hukuncin da aka zartar ranar Alhamis, mai shari’a James Omotosho ya ce hujjojin da masu gabatar da kara suka gabatar ciki har da bidiyoyin da Kanu ke furta barazanar tashin hankalin da suka hada da kira ga aikata miyagun ayyuka sun wadatar wajen tabbatar da laifin.

An ce sauran shari’o’in za su ci gaba yayin da kotu ta ce akwai karin bayanai da za su biyo baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here